U-23: Nigeria za ta fafata da Senegal

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Kasashe uku ne za su wakilci Afirka a wasannin Olympics da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa

Tawagar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria za ta kara da ta Senegal a wasan daf da karshe a gasar cin kofin Afirka ranar Laraba.

Senegal ce ke karbar bakuncin wasannin na cin kofin nahiyar Afirka da kuma samun gurbin kasashe uku da za su wakilci nahiyar a wasannin Olympics na badi.

Nigeria ta kai wannan matakin ne bayan da ta yi na biyu a rukuni na biyu da maki biyar, Senegal kuwa mataki na daya ta kammala da maki tara a rukunin farko.

Wasa na biyu na daf da karshe a gasar kuwa za a yi ne tsakanin Algeria wadda ta jagoranci rukuni na biyu da Afirka ta Kudu wadda ta yi na biyu a rukunin farko.

Za a buga wasannin neman mataki na uku a gasar da kuma wasan karshe a ranar Asabar.

Kasashe uku ne za su wakilci nahiyar Afirka a wasan kwallon kafa da za a yi a wasannin Olympics da Brazil za ta karbi bakunci a shekara mai zuwa.