Messi zai buga wasa da Bayern Leverkusen

Image caption Barcelona ta kai wasan zagayen gaba a gasar zakarun Turai

Lionel Messi ya shirya buga wa Barcelona wasan gasar cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Bayer Leverkusen a ranar Laraba.

Messi, dan kwallon Argentina ya buga wa Barcelona wasanni hudu ne tun lokacin da ya warke daga jinyar watanni biyu da ya yi.

Sai dai watakila Neymar ba zai takawa Barca leda ba a karawar sakamakon dan raunin da ya ji a wajen atisaye a ranar Talata.

Barcelona ba ta fayyace iya lokacin da Neymar zai yi jinya ba, kuma tuni Jeremy Mathieu da Sergi Roberto da Douglas da kuma Rafinha ke jerin 'yan wasa da suke jinya.

Shi kuwa Dani Alves ba zai buga fafatawar ba sakamakon hukuncin dakatar da shi da aka yi daga buga wasa.

Tuni dai Barcelona wadda ke rike da kofin ta samu gurbin shiga wasannin gaba na gasar, illa tana son kafa tarihin kasa doke ta a wasannin cikin rukuni, wanda rabon da ta yi hakan tun kakar 2011/12.