'Yan wasana sun yi rawar gani — Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Giroud ne ya ci kwallaye uku a karawarsu da Olympiakos.

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce 'yan wasan kulob dinsa sun mamaye baki daya wasan da suka buga da Olympiakos domin ganin sun kai mataki na 16 na gasar Zakarun Turai.

Mista Wenger ya ce, "wannan ce nasarar da ta fi kowacce a wasannin gasar zakarun Turai da kungiyarmu ta yi. Ina alfahari sosai."

Dan wasan gaba na Faransa Olivier Giroud ne ya ci dukkan kwallaye ukun da suka ci a a ranar Laraba.

Hakan na nufin Arsenal ta kai matakin sili daya kwale a matakin wasanni na kungiyoyin 16.