"'Yan hamayya na son a hada mu rukuni daya"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kowa na son ya zama a rukunin da za a sa Chelsea, in ji Morinho.

Kociyan Chelsea Jose Morinho ya ce abokan hamayyar kulob dinsa na son a hada su rukuni guda a gasar zakarun Turai.

Nasarar da kungiyar ta samu a kan Porto da ci 2-0 na nufin za ta zamo cikin rukuni guda da kungiyoyi shida da suka zo na biyu a rarraba rukunin da za a yi ranar Litinin.

Morinho ya ce "kungiyoyi da suka zo na biyu irin su Paris St-Germain da Juventus da PSV da Eindhoven da Benfica da Roma da kuma Gent duk na son ganin sun zo rukuni daya da mu."

Chelsea dai na sha da kyar a kakar wasannin Firimiyar Ingila na bana, amma kuma tana matukar kokari a gasar zakarun Turai.