Moses da Reid za su yi jinya a West Ham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Moses zai yi jinyar makonni shida

West Ham ta kara gamuwa da cikas bayan da 'yan wasanta Winston Reid da Victor Moses suka samu raunuka.

Kowannensu zai yi jinyar akalla makonni shida.

Bilic ya ce "Victor zai yi jinyar makonni hudu zuwa shida. Kuma cikas ne ga kungiyarmu."

Wasu daga cikin 'yan West Ham da ke jinya sun hada da Dimitri Payet da Diafra Sakho da kuma Manuel Lanzini.

Bilic kuma ya ce watakila Enner Valencia ba zai buga wasansu da Stoke ba duk da cewar ya yi jinyar makonni biyar.