Za a haramta wa Schweinsteiger buga wasanni uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bastian ya kama hannun hagun Reid a lokacin da suke jiran kwallo.

Za a haramta wa dan wasan tsakiya na Manchester United, Bastian Schweinsteiger buga wasanni uku bayan ya amsa laifin aikata ba daidai ba, kamar yadda hukumar kwallon kafar Ingila FA ta zarge shi.

An same shi da laifin ne bayan da ya kama hannun dan wasan West Ham Winston Reid, lokacin da suke jira su buga 'free-kick' a wasan da aka buga a filin Old Trafford ranar Asabar.

An dauki wannan laifi da ya aikata a hoton bidiyo.

Schweinsteiger mai shekaru 31 ba zai buga tamaula ba a karawar da za a yi da Bournemouth da Norwich da kuma Stoke, amma zai dawo daidai lokacin wasan su da Chelsea.