Bournemouth ta ci Manchester United 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An cire Manchester United daga gasar cin kofin zakarun Turai

Bournemouth ta doke Manchester United da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 16 da suka yi a ranar Asabar.

Bournemouth ta fara cin kwallo ta hannun Stanislas a minti na biyu da fara tamaula, inda United ta farke kwallon ta hannun Fellaini a minti na 24.

Tsohon dan wasan United Josh King shi ne ya ci wa Bournemouth kwallo ta biyu da hakan ya sa ta hada maki uku a wasan.

Manchester United tana da maki 29, yayin da Bournemouth ke da maki 16.

Bournemouth za ta buga wasan mako na 17 da West Brom, yayin da Manchester United kuwa za ta karbi bakuncin Norwich City.