Manchester City ta doke Swansea da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City ta dare mataki na daya a kan teburin Premier

Manchester City ta ci Swansea 2-1 a gasar Premier wasan mako na 16 da suka kara a filin wasa na Ettihad ranar Asabar.

Bony ne ya fara ci wa City kwallo a minti na 26 da fara tamaula, kuma Toure ya zura ta biyu bayan da kwallo ta bugi Iheanacho ta shiga raga.

Swansea kuwa wadda ta buga karawar ba tare da kociyanta Garry Monk wanda ta raba gari da shi a ranar Laraba ta zare kwallo daya ne ta hannun Gomis.

Da wannan sakamakon Manchester City ta dare mataki na daya a kan teburi da maki 32, ita kuwa Swansea tana matsayi na 15 da maki 14.

City za ta buga wasan mako na 17 da Sunderland, yayin da Swansea za ta karbi bakuncin West Brom.