Arsenal ta dare mataki na daya a teburin Premier

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsenal ta koma mataki na daya a kan teburin Premier

Arsenal ta hau kan teburin Premier, bayan da ta ci Aston Villa 2-0 a gasar Premier da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na Villa Park.

Arsenal wacce ta kai wasan zagayen gaba a gasar cin kofin zakarun Turai, ta fara cin kwallo ne ta hannun Olivier Giroud daga bugun fenariti a minti na takwas da fara wasa.

Aaron Ramsey ne ya ci wa Arsenal kwallo ta biyu saura minti bakwai a je hutun rabin lokaci, wanda hakan ne ya bai wa Arsenal maki uku a fafatawar.

Arsenal ta ci wasanni 10 a gasar Premier bana da hakan ya ba ta damar darewa matsayi na daya a gasar Premier.

Manchester City ce a mataki na biyu wadda Arsenal ta ba ta tazarar maki daya, sai kuma a ranar Litinin ce Leicester za ta kece raini da Chelsea.