Kamaru na neman sabon kociyan tamaula

Image caption A ranar Lahadi ce Kamarun ta tallata aikin horas da tawagar kwallon kafarta

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta tallata aikin horas da tawagar kwallon kafar kasar, domin maye gurbin Volker Finke wanda ta sallama a karshen watan Oktoba.

Hukumar ta saka tallan neman sabon mai horas da 'yan wasan tamaula ne a shafinta na Intanet a ranar Lahadi.

Tun lokacin da hukumar ta raba gari da Finke, a ranar 30 ga watan Oktoba ne ta nada Alexandre Belinga a matsayin kociyan rikon kwarya.

Tuni kuma Belinga, ya jagoranci kasar kaiwa wasan zagayen gaba a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, bayan da ya ci Nijar 3-0 haduwa biyu da suka yi.

Hukumar ta tsayar da ranar 15 ga watan Disamba domin rufe karbar takardun neman aikin horas da tawagar kwallon kafa ta Kamarun.