Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Bahagon Abba da Shagon Hafsat babu kisa a wannan takawar

Wasanni takwas aka fafata a damben gargajiya da aka yi a ranar Lahadi da safe a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Nigeria.

Dukkan wasannin da aka yi an ci 'yan kallo ne, bayan da babu dan damben da aka kashe a dukkan karawar da aka yi.

Sai dai kuma wasa tsakanin Shagon Idi daga Arewa da Autan Faya daga Kudu ya kayatar, haka ma fafatawa tsakanin Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Dan Kanawa daga Kudu.

Shi ma wasan Cika Guramada da Dan Sama'ila daga Kudu ya yi kyau matuka, haka ma gumurzu tsakanin Bahagon Dakaki daga Kudu da Fijot daga Arewa.

Bahagon Alin Tarara daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu sun fafata, aka kuma rufe wasan da dambatawa tsakanin Habu na Dutsen Mari da Shagon Aleka daga Kudu.