Gwarzon Afirka: Ayew da Aubameyang da Toure

Image caption A ranar bakwai ga watan Janairu za a sanar da zakaran bana a kwallon kafar Afirka

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta sanar da sunayen 'yan wasa uku da ke yin takarar lashe kyautar dan kwallon kafa na Afirka da ya fi yin fice a bana.

'Yan wasan da ta fitar sun hada da Andre Ayew na Ghana/ Swansea City da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon/ Borussia Dortmund da kuma Yaya Toure dan kwallon Cote d"Ivoire/ Manchester City.

Caf din ta bayyana sunayen 'yan wasan ne a ranar Litinin 14 ga watan Disamba a Abuja, Nigeria.

Haka kuma ta fitar da sunayen 'yan wasa uku da za a zabi wanda ya fi taka rawa da ke murza leda a gida na bana.

'Yan wasan sun hada da Baghdad Boundjah na Algeria/ Etoile du Sahel da Mbwana Aly Samata na Tanzania/ TP Mazembe da kuma Robert Kidiaba na jamhuriyar Congo/ TP Mazembe.

Masu horas da tamaula da daraktan tsare-tsare na mambobin kasashen hukumar kwallon kafar Afirka ne za su kada kuri'u.

A ranar bakwai ga watan Janairu ake sa ran sanar da wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ya fi yin fice da ke taka leda a Turai da wanda ke murza leda a gida na bana.