Messi na son lashe kofuna 5 a kakar bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ta dauki kofuna hudu a kakar wasan bana

Lionel Messi na fatan lashe kofin zakarun nahiyoyin duniya kuma kofi na biyar da yake son ya dauka a kakar wasannin bana.

Barcelona za ta kece raini da Guangzhou Evergrande, a wasan daf da karshe a ranar Alhamis a Yokohama.

Barcelona ta lashe kofin La Liga da na Copa Del Rey da na Zakarun Turai da kuma na Uefa Super Cup a kakar wasannin bana,

Barcelona ta taba daukar kofin zakarun nahiyoyin duniya a shekarar 2009 da kuma 2013.

A ranar 20 ga watan Disamba ne za a buga wasan karshe na gasar a Yokohama.