Leicester ta koma matakinta na daya a Premier

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Karo na tara kenan da aka ci Chelsea a gasar Premier bana

eLeicester City ta koma matakinta na daya a kan teburin Premier, bayan da ta doke Chelsea da ci 2-1 a gasar Premier da suka buga a ranar Litinin.

Jarmie Vardy ne ya fara ci wa Leicester kwallon farko kuma ta 15 jumulla da ya ci saura minti 11 a je hutun rabin lokaci, kuma bayan da aka dawo ne da minti uku Riyad Mahrez ya ci ta biyu.

Chelsea ta zare kwallo daya da aka zura mata ta hannun Loic Remy, kuma ta farko da ya zura a raga a gasar ta Premier.

Da wannan sakamakon Leicester City ta koma matakinta na daya a kan teburin Premier da maki 35, bayan da ta buga wasanni 16.

Chelsea kuwa tana mataki na 16 da maki 15, kuma karawa ta tara kenan da aka doke ta a gasar ta Premier, ta kuma ci wasanni hudu sanan ta yi canjaras a karawa uku.