Arsenal za ta hadu da Barcelona

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barcelona ce ta lashe gasar a kakar wasan da ta wuce

Arsenal za ta kara da Barcelona a zagaye na biyu na Gasar Zakarun Turai da za a buga a cikin watan Fabarairu.

Chelsea kuwa za ta fafata ne da Paris St-Germain a karo na uku a jere a wannan gasar, yayin da Manchester City za ta hadu da Dynamo Kiev.

Za a yi wasan farko ne a ranakun 16 da 17 da kuma 23 zuwa 24 ga watan Fabarairu sai kuma bugu na biyu a ranakun 8-9 da kuma 15-16 ga watan Maris.

Cikakken jadawalin:

  • Gent v Wolfsburg
  • Roma v Real Madrid
  • Paris St-Germain v Chelsea
  • Arsenal v Barcelona
  • Juventus v Bayern Munich
  • PSV Eindhoven v Atletico Madrid
  • Benfica v Zenit St Petersburg
  • Dynamo Kiev v Manchester City