Mourinho na zargin ana cin amanarsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier

Jose Mourinho ya yi zargin cewa wasu mutane suna cin amanar aikin da yake gudanarwa a Chelsea, bayan da Leicester City ta doke su 2-1 a gasar Premier ranar Litinin.

Chelsea - mai rike da kofin Premier - ta sha kaye a wasanni tara a cikin wasanni 16 da ta yi a gasar ta Premier.

Hakan ne ya sa Chelsea ta koma mataki na 16 a kan teburin gasar, kuma maki daya ya rage ta shiga sahun kungiyoyin da za su iya barin wasannin Premier.

Mourinho ya ce, "Daya daga cikin kwarewar da nake da ita shi ne iya karanta wasan tamaula na kuma sanar da 'yan wasa na, ina jin kamar ana cin amana ta".

"Wani abin farin ciki na taka rawar gani a bara a Chelsea, na kuma kai wasu 'yan wasa matsayin da ba za su iya kaiwa ba, amma sun kasa kula da hakan", in ji Mourinho .

Wasanni uku kacal aka ci Chelsea wadda ta lashe kofin Premier na bara, sannan ta bai wa Manchester City tazarar maki takwas wadda ta kammala a mataki na biyu.