Uefa: Ba Messi da Neymar da Suarez a 'yan wasa 11

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Messi da Neymar suna cikin 'yan takarar Ballon d'Or

'Yan wasan Barcelona, Messi da Neymar da Suarez ba sa cikin 'yan wasa 11 fitattu na Gasar cin kofin Zakarun Turai da aka shiga zagaye na biyu a gasar.

'Yan wasan uku sun zura kwallaye 10 jumulla, wanda hakan ya sa Barcelona ce ta fara kaiwa wasan zagaye na biyu a gasar.

Kuma tsakanin Messi da Neymar da Suarez sun ci kwallaye 46 a dukkan wasannin da suka buga a kakar wasan bana.

Messi da Neymar suna cikin 'yan takarar lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ya fi yin fice a bana, wato Ballon d'Or.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid shi ne yake rike da Ballon d'Or na shekarar bara.