Vardy da Mahrez ba na sayarwa bane - Ranieri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester City ta koma mataki na daya a kan teburin Premier

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri, ya ce Jamie Vardy da kuma Riyad Mahrez ba na sayarwa bane, bayan da kungiyar ta dare mataki na daya a teburin Premier.

A ranar Litinin ne Leicester da doke Chelsea 2-1 a gasar Premier wasan mako na 16, kuma Vardy ne ya ci kwallon farko kuma ta 15 jumulla, Mahrez ya ci ta biyu kuma ta 11 da ya zura a raga a bana.

Ranieri ya ce babu kungiyar da za ta iya daukar Vardy da Mahrez, domin basu da kudaden da za su iya daukarsu, basu ma da farashi, idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula a watan Janairu.

Vardy ya koma Leicester City a shekarar 2012 kan kudi fam miliyan daya, yayin da Mahrez ya koma kungiyar a shekarar 2014 kan kudi fam 400,000.

A bara a gasar Premier bayan da aka buga wasanni 16, Leicester wadda Nigel Pearson ke horas da ita a lokacin tana mataki na karshe ne a gasar.