Ana tattauna makomar Mourinho a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho na fuskantar matsin lamba

Shugabanni a kungiyar Chelsea, sun soma tattauna makomar kocin tawagar Jose Mourinho.

Mai kungiyar, Roman Abramovich ya gana da wasu 'yan kwamitin zartarwar kungiyar bayan da aka doke Chelsea a wasanni tara cikin 16.

A yanzu dai maki daya tal ne ya raba Chelsea da kungiyoyin da za su iya nitsewa daga gasar.

Babu tabbas a kan ko Mourinho zai ci gaba da jan ragamar kungiyar ko kuma za a raba gari.

A makonnin baya, Abramovich ya nuna goyon bayansa ga Mourinho amma a yanzu babu tabbas.