Platini ba zai halarci zama da kwamitin Fifa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwamitin da'a na hukumar Fifa ne ya shirya jin bahasi daga Blatter da Platini

Lauyoyin Michel Platini, sun ce ba zai halarci zaman kwamitin kula da da'ar hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ba da za a yi ranar Juma'a.

Lauyoyin sun ce tuni aka riga aka yanke hukunci, kuma wannan ya shiga hakkin wanda ba shi da laifi.

Yanzu haka an dakatar da Mista Platini da shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter daga shiga harkokin tamaula kwanaki 90 a watan Oktoba.

Kwamitin kula da da'a na hukumar Fifa na yin bincike kan cin hanci.

Dukkansu biyun sun musanta yin abin da ba daidai ba.