An bai wa Eto'o damar zama kociyan tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Eto ya taka leda a Barcelona da Inter Milan da Anzhi Makhachkala da Chelsea da Everton

Kungiyar Antalyaspor ta Turkiya ta nada Samuel Eto'o a matsayin kociyan rikon kwarya, bayan da yake murza leda a kungiyar.

Eto'o mai shekara 34, ya koma Antalyaspor kan yarjejeniyar shekaru uku a cikin watan Yuni, an kuma bashi wasanni uku domin ya nuna kansa idan zai iya aikin.

Eto'o ya maye gurbin Yusuf Simsek wanda ya amince da raba gari da kungiyar a ranar bakwai ga watan Disamba.

Antalyaspor za ta yanke shawara idan za ta bai wa Eto'o aikin horas da 'yan wasanta na dindindin a nan gaba.

Eto'o tsohon dan kwallon Kamaru zai yi aiki ne tare da daraktan wasannin kungiyar Mehmet Ugurlu.