Saliyo ta kaucewa fushin Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saliyo ta kaucewa dakatar da ita da Fifa ta shirya yi

Saliyo ta maido da shugabannin hukumar kwallon kafa da ta rusa a baya, domin kaucewa hukuncin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa.

Saliyon ta yanke wannan hukuncin ne a ranar Laraba a taron da shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya jagoranta.

Fifa ta bai wa Saliyo wa'adin dawo da jami'an kwallon kafar kasar da ta rusa kafin 16 ga watan Disamba, idan ba haka ba a hana kasar shiga sabgogin tamaula a duniya.

A makon jiya ne hukumar wasanni ta Saliyo ta rusa hukumar kwallon kafar kasar wadda ke cin gashin kanta wadda Isha Johansen ke jagoranta.

Saliyo ta ce ta rusa mahukuntan kwallon kafar kasar ne, bayan da Isha Johansen, ta soke kwamitin mutane bakwai da aka kafa domin zabo mutanen da za su halarci taron hukumar kwallon kafar kasar da za a yi.

Sai dai kuma Fifa ta ce hukumar kwallon kafa ta kasa mai cin gashin kanta ce, bai kamata gwamnati ta yi katsalandan cikin harkokinta ba.