Tennis: Amarya za ta buga wasa ranar aurenta

Image caption Sai da dai abokiyar karawarta ta amince sannan aka sauya lokacin.

Arina Rodionova za ta fi yawancin amare yin hidima a ranar aurensu saboda tana son samun cancantar shiga gasar Australian Open.

'yar wasan mai shekaru 26 za ta buga wani wasan neman cancantar shiga rukunin wadanda za su buga gasar Grand Slam ta shekara mai zuwa ne ranar Assabar da safe kafin a daura ma ta aure da rana.

Arina haifaffar kasar Rasha na bukatar ta ci wasanni biyu domin samun cancantar shiga gasar wadda za a soma ranar 18 ga watan Janairu.

Da dai da rana ne za ta buga wasan da Storm Sanders amma sai lokacin ya zo daidai da lokacin aurenta da wani dan wasan kwallon kafa Ty Vickery, abin da ya sa aka mayar da wasan da safe.

Karin bayani