Chelsea ta kori Jose Mourinho

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Chelsea ba ta taka rawar gani ba a kakar wasan Premier ta bana.

Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta kori kocinta, Jose Mourinhou daga aiki watanni bakwai bayan ya jagorance ta wajen lashe kofin Gasar Premier.

Dan kasar Portugal din, mai shekaru 52 a duniya, yana tsaka da yin wa'adinsa na biyu ne a kungiyar, bayan ya karbi ragamar horas da 'yan wasanta a shekarar 2013.

Kungiyar Chelsea ta kammala kakar wasan Premier da ta wuce da maki takwas kan kungiyar da ke biye mata, kuma ta lashe kofin League, sai dai a kakar wasa ta bana kungiyar ta shiga halin tsaka mai wuya, inda ta yi asarar maki tara a cikin wasanni 16 da ta buga.

Wasa na karshe da Mourinho ya jagoranta shi ne wanda kungiyar Leicester City ta doke su da ci 2-1.

Ana sa ran za a maye gurbinsa da ko dai Pep Guardiola ko Guus Hiddink ko Brendan Rodgers ko kuma Juande Ramos.