Ba alamun sallamar Mourinho -Nevin

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea za ta ziyarci Sunderland a gasar ta Premier ranar Assabar

Tsohon dan wasan kungiyar Chelsea Pat Nevin ya ce bai ganin yiwuwar za a sallami manajan kungiyar, Jose Mourinho, daga aiki.

Akwai rashin tabbas game da makomar Mourinho a kulob din sakamakon wata tattaunawa da daraktocin kulob din suka yi a kansa.

Kulob din, mai rike da kambun gasar Premier ya sha kashi da ci 2-1 ranar Litinin a hannun Leicester wadda ita ce ta tara a wasanni 16 da ta buga a kakar gasar ta bana, abin da ya sa ya zama maki biyu ne kawai suka rage masa ya fita daga rukunin zakarun kungiyoyi.

Sai dai a yayin da yake zantawa a cikin wani shiri na musamman da gidan radiyon BBC Radio 5 live ya gabatar, Nevin ya ce jita-jita game da makomar Mourinho ba sabon abu ba ne kuma za ta bi shanun sarki.

Karin bayani