Hiddink zai zama kocin Chelsea

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hiddink ya taba zama kocin riko a Chelsea inda ya lashe gasar FA a shekarar 2009.

Tsohon kocin Netherlands, Guus Hiddink na gab da zama kocin riko a kungiyar Chelsea bayan da aka kori Jose Mourinho.

Dan shekaru 69, a yanzu haka yana tattaunawa da wasu jami'ai na Chelsea a London.

Hiddink ya taba zama kocin riko a Chelsea inda ya lashe gasar FA a shekarar 2009.

An kori Mourinho ne watanni bakwai bayan da ya lashe gasar Premier tare da kungiyar ta Chelsea

A yanzu haka dai maki daya ne tal ya raba Chelsea da kungiyoyin da za su iya nitsewa kasa su koma gasar Championship.