Real Madrid ba ta zawarcin Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya taba lashe kofi a Real

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya ce a yanzu haka dai kungiyar ba ta tunanin dauko Jose Mourinho.

Mourinho mai shekaru 52, ya lashe gasar La Liga da kuma na Copa del Rey a lokacin da ya ja ragamar Real daga 2010 zuwa 2013.

A ranar Alhamis ne Chelsea ta kore shi daga aiki.

Kocin Real, Rafael Benitez na fuskantar matsin lamba tun bayan da Barcelona ta lallasa Real da ci hudu da nema a Bernebeu.

Perez ya ce "Babu wanda ya san gobe, amma a yanzu dai ba zai zo Madrid ba."