Norwich ta doke Man United 2-1 a Old trafford

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man United ta koma mataki na biyar a kan teburi

Magoya bayan Manchester United sun yi wa 'yan wasa kuwwa bayan da aka tashi wasan Premier da Norwich City ta doke ta da ci 2-1 a Old Trafford.

Duk da United ce ta fi taka leda a karawar bai hana Norwich zura kwallon farko ta hannun Cameron Jerome kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne Norwich ta kara kwallo ta biyu a ragar United ta hannun Alex Tettey.

United ta zare kwallo daya ne ta hannun Anthony Martial, sai dai kuma karo na shida kenan da kungiyar ta kasa yin nasara a wasannin da ta yi.

Hakan ne ya kuma kara matsi ga kociyan United Manchester United Louis Van Gaal, wanda tuni ake ta kiraye-kirayen a kore shi daga Old Trafford.