Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Kada Mutsa daga Arewa da Matawallen kwarkwada daga Kudu

An buga damben gargajiya guda biyar da yammacin Asabar a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

An fara ne da fafatawa tsakanin Shagon Tirabula daga Kudu da Shagon Lawwalin Gussau, inda Shagon Lawwalin Gusai ya yi kisa a turmi na biyu.

Karawa tsakanin tsakanin Shagon Jimama daga Kudu da Shagon Musan Kaduna ta kayatar matuku, kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba damben.

Daga nan ne aka shiga fili tsakanin Yellow dan Gusau da Shagon Shagon Bahagon Fandam, kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba wasan.

A wasan karshe a filin kuwa Shagon Shagon Faya ne daga Kudu ya kashe Shagon Buzu daga Arewa a turmi na biyu.

Sai a ranar Lahadi safe da yammaci ake sa ran dambatawa a wasanni da dama.