Guardiola zai bar Munich a karshen kakar bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Guardiola ya koma Munich da horas da tamaula a 2013

Pep Guardiola zai bar Bayern Munich a karshen kakar wasan bana, kuma Carlo Ancelotti ne zai maye gurbinsa a kungiyar.

Ana kuma rade-radin cewar zai koma horas da tamaula ne a Manchester City ko Manchester United ko Chelsea ko kuma Arsenal.

Guardiola wanda ya koma Munich a shekarar 2013, ya lashe kofunan Jamus biyu da kuma na Kalubalen kasar.

Carlo Ancelotti wanda yake yin hutu tun bayan da Real Madrid ta sallame shi a watan Mayun 2015, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da Bayern Munich.

Munich wadda ta bayar da tazarar maki takwas a gasar Bundesliga da za a je hutu, za kuma ta fafata da Juventus a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai.