Dan Kanawa ya dambata da Alin Tarara

Image caption Wannan takawar da suka yi babu kisa a turmi uku da suka yi

Wasannin 10 aka yi da sanyin safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Cikin karawa 10 da aka fafata guda biyu ne aka yi kisa da ya hada da wasan da Shagon Buzu daga Arewa ya kashe Bahagon Bakura daga Kudu a turmi na uku.

Haka ma Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa ya buge Mai Gaban Karo daga Kudu a turmin farko.

Sauran wasannin da suka kayatar da ba a yi kisa ba sun hada da wasa tsakanin Shagon Musan Kaduna da Shagon Bahagon Fandam daga Kudu.

Wasan Sanin Kawo daga Arewa da Shagon Shagon Faya daga Kudu ya yi armashi, haka ma karawa tsakanin Sanin Kwarkwada daga Kudu da Obi Shagon Dogon Sani.

Gumurzu da aka yi tsakanin Dan Kanawa daga Kudu da Alin Tarara daga Arewa an biya 'yan kallo kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba dambe.

An kuma yi wasa tsakanin Shagon Idi daga Arewa da Shagon Autan Faya da kuma na Kurarin Kwarkwada daga Kudu da Dogon Na Manu daga Arewa babu kisa.

An kuma sa zare tsakanin Shagon Autan Tirabula daga Kudu da Aljani Mai Carbi daga Arewa kuma turmi biyu suka yi babu wanda ya je kasa aka raba su.