Madrid ta kaskantar da mu in ji kociyan Rayo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana mataki na uku a kan teburin Premier

Kociyan Rayo Vallecano, Paco Jemez, ya ce lallasawar da Real Madrid ta yi musu da ci 10-2 ranar Lahadi a gasar La Liga, tamkar kaskantar da kuma azabtar da su ne.

Gareth Bale ne ya ci kwallaye hudu rigis sannan Karim Benzema ya ci uku a karawar da Rayo ta kammala da 'yan wasa tara a cikin fili a Bernabeu.

Jemez ya ce gasar kwallon Spaniya ta fuskanci koma-baya sakamakon abin kunyar da aka yi a La Liga a ranar Lahadin.

Ya kara da cewar suna jin an kaskantar da su, kuma hakan ba zai amfani Madrid ko kuma kwallon Spaniya ba, yana mai cewa "Hakika gasar ta fuskanci kalubale".

Ya kuma ce mutane da dama ba su yi farin ciki da abubuwan da suka faru a karawar ba, ganin cewa lamarin ya faru ne a gasar da ta fi yin fice a duniya.