Zamalek ta fice daga gasar Masar kan alkalanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mahukuntan Zamalek za su sake zama taro kan batun

Mai rike da kofin gasar kwallon kafa ta Masar, Zamalek ta bayar da sanarwar ficewa daga wasannin kasar da take fafatawa ta bana.

Mahukuntan kungiyar ne suka cimma wannan matsaya, bayan da ta sha kaye a hannun El-Gaish 3-2 a gasar kasar da suka yi a ranar Lahadi.

Sai dai kuma hukumar kwallon kafar kasar ta ce ba ta samu wata sanarwa ko kuma sako daga kungiyar ba.

Zamalek na bukatar a gyara yadda alkalan gasar ke gudanar da aikinsu musamman a lokacin da take yin wasanninta.

Zamalek ta bukaci a sauya alkalin wasa Mahmoud Al Banna wanda ya jagoranci karawar tun kafin su fafata a gasar.

Minti biyu kuma da fara wasan Al Banna ya bai wa mai tsaron bayan Zamalek, Ali Gabr jan kati ya kuma bai wa El-Gaish fenariti har guda biyu a wasan.

Dokar hukumar kwallon kafar Masar ta ce duk kungiyar da ta fice daga gasar kasar don radin kanta, za a maida ita buga wasannin 'yan rukuni na hudu.