Doke City ya kara mana kwarin gwiwa - Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce doke Manchester City da suka yi ya kara musu kwarin gwiwar cewar suna daga cikin kungiyoyin da za su iya daukar kofin Premier.

Arsenal ta doke Manchester City ne da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 17 da suka fafata a ranar Litinin.

Gunners wadda ba a doke ta ba a wasanni shida da ta buga a jere tana mataki na biyu a kan teburi da maki 32, ta kuma kai wasan zagaye na biyu a gasar kofin zakarun Turai.

Wenger ya ce "Nasarar da muka samu ta karfafa mana gwiwa da kuma yarda da cewar za mu iya daukar kofin Premier ta bana".

Rabon da Arsenal ta dauki kofin Premier tun a shekarar 2004.

Arsenal din za ta ziyarci filin wasa na St Mary domin karawa da Southampton a wasan mako na 18 a ranar Asabar.