Platini ya zargi Fifa da rashin iya aiki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Litinin ne Fifa ta dakatar da Blatter da kuma Platini

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Michel Platini, ya zargi kwamitin da'a na Fifa da yin barcin shekara hudu, bayan da aka dakatar da shi daga shiga harkokin kwallon kafa tsawon shekara takwas.

Kwamitin ya dakatar da Platini da kuma Sepp Blatter daga shiga harkokin kwallon kafa bisa zargin karbar sama da fam miliyan daya daga hannun Sepp Blatter a shekarar 2011.

Dukkansu sun musanta zargin, suna mai cewa za su daukaka kara kan lamarin.

A hirar da aka yi da shi a wata kafar yada labarai ta Faransa, Platini, ya yi tambaya kamar haka: me kwamitin da'ar yake yi a lokacin da aka ba shi kudaden daga tsakanin 2011 zuwa 2015, suna barci kenan ?

Ya kuma kara da cewar, "Sai yanzu ne suka farka a lokacin da ake shirye-shiryen zaben shugabancin Fifa, kuma a lokacin da nake takara? Wannan abin mamaki ne".