Zamalek ya yi amai ya lashe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zamalek din ya bukaci da a gyara yadda ake alkalancin gasar kasar

Kulob din Zamalek, mai rike da kofin gasar kwallon kafar Masar, ya ce zai ci gaba da buga gasar, bayan da ya bayar da sanarwar ficewa daga gasar a ranar Lahadi.

Zamalek ya ce ya fice ne daga gasar bisa rashin adalcin da ya yi zargin an yi masa a karawar da El-Gaish ta doke su 3-2 a wasan gasar kasar.

A ranar Litinin ne mahukuntan gasar suka yi taro suka kuma fitar da sanarwar za su ci gaba da fafatawa a gasar ta Masar.

Hukumar kwallon kafar Masar ta ce za a dakatar da duk kungiyar da ta fice daga gasar daga shiga tamaula tsawon shekara daya, sannan ta koma buga gasar 'yan rukuni na hudu.

Zamalek ya rubuta wasikar korafi ga hukumar kwallon kafar kasar bisa yadda alkalin wasa Mahmoud Al Banna ya jagoranci karawar da suka yi da El-Gaish.

Kuma tun kafin wasan Zamalek, ya bukaci a sauya alkalin wasan saboda suna zargin ba zai yi musu adalci ba.

Minti biyu kuma da fara wasan Al Banna ya bai wa mai tsaron bayan Zamalek, Ali Gabr, jan kati ya kuma bai wa El-Gaish fenariti har guda biyu a wasan.