"Magana kan Van Gaal rashin girmamawa ne"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester United ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier

Kociyan Arsenel, Arsene Wenger, ya ce rade-radin da ake yi kan makomar Louis van Gaal a Manchester United tamkar rashin girmamawa ce.

Rahotanni na cewa matsayin Van Gaal a Manchester United na kila wa kala, bayan da ya kasa cin wasa a karawa shida da ya yi a jere.

A makon jiya ne aka sallami Jose Mourinho daga aikin horas da Chelsea, ana kuma cewa shi ne zai maye gurbin Van Gaal a Old Trafford.

Wenger ya ce, "Ba na kaunar wani ya rasa aikinsa, a koda yaushe ina jin bacin rai idan hakan ta faru".

Van Gaal ya fada bayan da aka tashi daga karawar da Norwich ta ci su 2-1 a gasar Premier cewar ya damu da halin da ya tsinci kansa a United.