Skrtel zai yi jinyar makonni shida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana mataki na tara a kan teburin Premier

Kulob din Liverpool ya tabbatar da cewar mai tsaron baya Martin Skrtel, zai yi jinyar makonni shida.

Skrtel ya ji rauni ne a karawar da Watford ta ci Liverpool 3-0 a gasar Premier wasan mako na 17 a ranar Lahadi.

Dan kwallon ya buga wa Liverpool wasanni 26 a dukkan wasannin da ta buga a bana.

Liverpool din tana mataki na tara a kan teburin Premier da maki 24, za kuma ta kara da Leicester a wasan mako na 18 a ranar Asabar.