Osimhen ya ce ba zai yi gaggawa ba

Image caption Osimhem ya haskaka a gasar da aka buga a Chile

Victor Osimhen wanda ya fi kowanne dan kwallo zura kwallaye a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 17, ya ce ba zai yi gaggawar zaben kungiya ba.

A yanzu yana murza leda tare da Ultimate Strikers a Lagos, amma ya shafe gajeren lokaci tare da Wolfsburg a Jamus sannan kuma zai ziyarci Arsenal.

Osimhen wanda zai cika shekaru 17 a ranar 29 ga watan Disamba, ya zura kwallaye 10 inda ya taimakawa Nigeria ta lashe kofin gasar 'yan kasa da shekaru 17 a watan Oktoba.

"Na ji dadin ziyarar da na kai Wolfsburg kuma zan ziyarci Arsenal, amma ba na gaggawa," in ji Osimhen.

A bisa dokokin Fifa dai, Osimhem ba zai iya kulla yarjejeniya ba da wata kungiya a Turai, har sai ya cika shekaru 18.