Ni da kaina zan bar Man United - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man United ta koma mataki na 6 a kan teburin Premier

Louis van Gaal ya ce shi da kansa zai bar aikin horas da Manchester United, ba sai an sallame shi ba.

Kociyan ya fadi haka ne a lokacin da yake ganawa da 'yan jaridu, bayan da suka yi masa tambaya kan makomarsa a Old Trafford.

Stoke City ce ta doke Manchester United da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 18 da suka fafata a ranar Lahadi.

United ta buga wasanni bakwai ba ta samu nasara ba, kuma 'yan jaridu sun tambayi Van Gaal idan yana fargabar zai rasa aikinsa.

Van Gaal ya ce batun da zai tattauna da babban jami'in United, Ed Woodward kenan ba da 'yan jaridu ba, domin fayyace zamansa a Old Trafford.