Man City ta zazzagawa Sunderland kwallaye 4-1

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mancity tana mataki na uku a kan teburin Premier

Manchester City ta ci Sunderland 4-1 a gasar Premier wasan mako na 18 da suka yi a filin wasa na Ettihad a ranar Lahadi.

Raheem Sterling da Yaya Toure da kuma Wilfried Bony ne suka ci wa City kwallaye uku tun kafin aje hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Kevin de Bruyne ya kara ci wa City kwallo ta hudu, daga nan kuma Sunderland ta zare kwallo guda ta hannun Fabio Borini.

Wilfred Bony ya buga fenariti amma kwallo ta yi sama, haka kuma kyaftin din City Vincent Kompany ya ji rauni a karawar minti daya kacal da shiga fili.

Komapany ya yi fama da jinyar da ta hana shi buga wa City wasanni takwas a baya.