Stoke City ta doke Man United 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester United tana nan da makinta 29 a kan teburi

Stoke City ta ci Manchester United 2-0 a gasar Premier wasan mako na 18 da suka kara a ranar Lahadi.

Stoke ta ci kwallon farko ne ta hannun Bojan Krkic, bayan da dan wasan United Memphis Depay ya yi kokarin bai wa David De Gea kwallo da ka.

Marko Arnautovic ne ya ci wa Stoke kwallo ta biyu, bayan da Bojan ya yi bugun tazara kuma kwallo ta bugi 'yan wasan United.

Wannan shi ne karo na hudu da aka doke United a wasan Premier a jere kuma tana nan da makinta 29.

Ita kuwa Stoke City ta hada maki 26 daga wasanni 18 da ta buga a gasar ta Premier.