Tottenham na haskakawa a gasar Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Spurs na murnar doke Watford

Tottenham ta taka rawar gani a gasar Premier ta Ingila da aka buga a ranar Litinin, inda ta bi Watford har gida ta kuma doke ta da ci biyu da daya.

Lamela da Son Heung-min ne suka ci wa Tottenham kwallayenta, a yayin da Ighalo ya ci wa Watford kwallo.

A yanzu Tottehnam ta koma matsayin na uku a kan tebur, har zuwa lokacin da Manchester City za ta buga na ta wasan.

Ita ma Everton ta sha kashi a gidanta bayan da Stoke ta doke ta da ci hudu da uku.

Sakamakon wasannin da aka buga:

  • Crystal Palace 0-0 Swansea
  • Everton 3-4 Stoke
  • Norwich 2-0 Aston Villa
  • Watford 1-2 Tottenham
  • West Brom 1-0 Newcastle