An haɗe mana kai — Benitez

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Benitez na fuskantar rashin tabbas a Real

Kocin Real Madrid, Rafael Benitez ya ce ana yin 'kamfe' na batanci a kansa da kuma kungiyar.

Benitez na fuskantar matsin lamba, tun bayan da Barcelona ta lallasa su da ci hudu da nema a watan da ya wuce.

"Akwai kamfe mara kyau a kan shugabanmu Florentino Perez da Real Madrid da kuma ni," in ji Benitez.

Benitez ya maye gurbin Carlon Ancelotti a farkon kakar wasa ta bana, inda Perez ya bayyana shi a matsayin "mutumin da ke shakar kwallo".

Benitez ya kara da cewar "Babu matsala a dangantaka tsakani na da 'yan wasa kuma ina da gogewa a fannin horas da 'yan wasa."