Duarte ya sake koma wa Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Angulu ta koma gidanta na tsamiya

Dan kasar Portugal, Paulo Duarte ya sake koma wa tawagar kasar Burkina Faso a karo na biyu a matsayin koci.

Ya maye gurbin Gernot Rohr, mutumin da ya koma gida domin kama aiki tare da hukumar kwallon kasar Jamus.

Duarte, mai shekaru 46, ya jagoranci Burkina Faso daga shekarar 2008 zuwa 2012, inda ya tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika.

Bayan da ya bar Burkina Faso, ya koma Gabon inda ya shafe 'yan watanni kafin su raba gari.