Babu hujjar yin murabus - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Van Gaal na cikin tsaka mai wuya

Kocin Manchester United, Louis van Gaal ya ce ba zai yi murabus ba, bayan da suka tashi babu ci tsakaninsu da Chelsea a ranar Litinin.

A yanzu United ta buga wasanni takwas kenan a jere, ba tare da samun nasara ba, kuma wannan ne karon farko da kungiyar ta fuskanci irin wannan matsalar tun a shekarar 1990.

'Yan wasan Manchester Juan Mata da Anthony Martial duk sun daki turke da kwallo a lokacin wasan.

Van Gaal ya ce "Idan 'yan wasa sun nuna kwazo, babu hujjar yin murabus."

Bayan da Stoke ta doke Red Devils da ci biyu da nema, sai aka soma sayar da wani kyalle mai sunan Jose Mourinho a wajen filin Old Trafford.