"Chelsea ta dauki 'hanyar' samun nasara"

Image caption Mikel ya ce babu tabbas a kwallon kafa

Dan kwallon Nigeria, John Mikel Obi ya ce Chelsea ta dauki hanyar samun nasara, bayan da suka buga wasanni uku ba tare da an doke su ba.

Tun bayan da aka kori Jose Mourinho, babu kungiyar da ta samu galaba a kan Chelsea.

Mikel ya ce zuwan Guus Hiddink a matsayin kocin riko, zai taimaki kungiyar.

"Komai ya canza tun da aka canza manaja," in ji Mikel.

Ya kara da cewa "Jose gogaggen koci ne, amma babu tabbas a kwallon kafa."

Chelsea wacce ta lashe kofin gasar Premier a watan Mayu, ta raba gari da Mourinho ne a ranar 17 ga watan Disamba bayan da kungiyar ta fuskanci rashin tabbas.