Aston Villa na zawarcin Remy daga Chelsea

Hakkin mallakar hoto fc chelsea
Image caption Remy na dumama benci a Chelsea

Kocin Aston Villa, Remi Garde ya ce zai yi kokarin sayen dan kwallon Chelsea, Loic Remy a matsayin aro, idan an bude kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Junairu.

Garde na kokarin ya kara wa tawagarsa kafin, a yayin da Villa ke matakin na karshe a kan teburin gasar Premier.

"Loic na musamman ne saboda ya san gasar kuma zai kara mana karfi," in ji Garde.

Remy ya koma Chelsea ne daga QPR a bara a kan fan miliyan 10 da rabi.

Amma kuma wasa daya tal aka soma tare da shi a kakar wasa ta bana, inda ya zura kwallo daya gasar Premier sannan ya ci kwallaye biyu a gasar kofin League.