Chelsea: Falcao zai ci gaba da jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Falcao yana jinya kuma ba zai dawo murza leda ba sai tsakiyar watan Junairu.

Mai taka leda a Chelsea Radamel Falcao ba zai dawo daga jinya ba har sai tsakiyar watan Janairu saboda rauninsa ya dagule.

Chelsea ta aro Falcao mai shekaru 29, daga kulob din kasar Monaco, amma rabonsa da murza leda, tun bayan kashin da suka sha a hannun Liverpool da ci 3-1 ranar 31 a watan Oktoba.

Kociyan rikon kwarya na Chelsea, Guus Hiddink ya ce Falcao ya yi ta samun rauni a cinyarsa a lokacin horo, kuma zai bukaci kwanaki goma kafin ya samun damar iya murza leda.

Ya ce, "A ganina mun samu koma baya ne. Mun sa shi a wani wasa, amma kuma ciwon dake cinyarsa ya ta'azzara, don haka sai ya kwana goma kafin ya iya buga wasa".

Manchester ta ari Falcao a kakar wasannin bara, kuma ya buga wa Chelsea wasannin gasar firimiya tara, inda ya ci kwallo daya kacal.