Sunderland za ta dauki Kone

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland na shirin kara karfin tawagarsa

Kocin Sunderland, Sam Allardyce na shirin sayen dan kwallon Ivory Coast, Lamine Kone.

Mataimakin shugaban kungiyar, Alex Hayes ya ce sun amsa tayin dan wasan mai shekaru 26.

Kone ya buga wa Faransa kwallo a matakin 'yan kasa da shekaru 20, amma ya koma buga wa Ivory Coast wasa a shekara ta 2014.

Hayes ya ce "A yanzu ya rage ga Lamine ya kulla yarjejeniya da Sunderland idan an gwada lafiyarsa."

Allardyce ya samu nasara a wasanni uku daga cikin 10 da ya jagoranci Sunderland.